30 Nuwamba 2015 - 08:17
Wani dan kunar bakin wake ya halaka a Iraki

Wani dan kunar bakin wake da ake kyautata zaton da Da’ish ne ya halaka kan sa a yayin da yake kokarin kai hari ga masu tattaki Arba’in daga Bagadad zuwa Karbala.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s}-abna-jami’an tsaron Iraki sun gano wani dan kunar bakin wake wanda yake shirin kai hari a kan masu tattakin arba’in a kan hanyar su ta Bagadad zuwa Karbala, maharin ya halaka kansa kafin ya samu sa’ar shiga sahun masu tattakin.

An dai tsaurara matakan tsaro a kan hanyoyin zuwa Karbala inda miliyoyin mutane ke tattaki domin halarta taron Arba’in na Imam Hussain{a.s}.288